Kimiyya Da Fasaha

Yadda aka Gudanar da Babban Taron Intanet na Duniya

Daga: Abdulrazaq Yahuza Jere

A rabar Larabar da ta gabata ne shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping ya miƙa saƙon taya murna ga babban taron intanet na Duniya na bana da aka yi a garin Wuzhen ta hanyar Bidiyo.

Xi, ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, sabon zagaye na juyin-juya-halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen Masana’antu na samun bunƙasa cikin sauri, kuma ana samun sabbin fasahohi irin su Fasahar Ƙirƙirarriyar Basira, waɗanda suka ƙara inganta ƙarfin fahimtar ɗan’Adam da sauya fasalin Duniya, ko da yake lamarin ya kuma zo da kasada da sauran ƙalubalen da ba a zata ba.

Shugaba Xi, ya ce ya kamata a fahimci yanayin fasahar zamani gaba ɗaya, da hanyoyin sadarwa da ci gaban fasaha, da ɗaukar sabbin ƙirƙire-ƙirƙire a matsayin ƙarfin gudanarwa na farko, sannan tsaro a matsayin ginshiƙi, da ci gaba mai haɗaka a zaman neman mutuntawa, kana a haɓaka ɓullo da sabbin abubuwa cikin hanzari, da samar da aminci a harkokin intanet da kuma yin aiki tare don samar da kyakkyawar makoma ta fasahar zamani.

Shugaban ya ƙara da cewa, ƙasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran ƙasashe, wajen ɗaukar mataki da zai kafa tarihi a ɓangaren juyin-juya-halin Fasahar Sadarwa, da gina al’umma mai makoma mai kyau a bangaren harkokin Intanet da kuma sanya Intanet ɗin ya zama mai amfani ga Jama’a da Duniya baki ɗaya.

An buɗe babban taro na Duniya a kan intanet na shekarar 2024 na Wuzhen, a wannan makon ne a garin Wuzhen da ke birnin Tongxiang na lardin Zhejiang, mai taken “Rungumar kyakkyawar makomar ɗan’Adam ta fasahar zamani mai kaifin basira-aiki tare don gina al’umma mai makoma mai kyau a ɓangaren harkokin intanet.”

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa Daga: Amina Xu An gudanar