Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a ƙarshen karni na 19 (Scramble for Africa), ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani, ‘Addis Ababa’ a 1886.

Mahaifin Taytu shi ne Ras Betul Haile Maryam, ya na cikin dangin Semien da ke mulki da suka yi iƙirarin zama zuriyar Daular Annabi Sulemanu AS ta hannun Sarkin Sarakuna Susenyos I. Kawun Taytu, shi ne shahararren jarumin ƙabilar Amhara, Wube Haile Maryam, wadda shi ne Hakimin Lardi sannan kuma mai ci kuma mai mulkin Larduna; Tsegede, Weilkat Tigray da kuma Eritrea. Mahaifiyar Taytu, Yewibdar, ta fito daga wani babban jigo a yankin Gonder.

Ilimi

Babu wasu bayanai da suka nuna cewa, Sarauniya Taytu ta halarci Makaranta; Duk da haka, an koya mata karatu da rubutu cikin harshen Amharic da Ge’ez.

Wannan abu ne mai wuyar gaske, ganin cewa a cikin wannan lokaci da wuya Mata su sami Ilimi. An yi imanin cewa an koyar da ita Diflomasiyya, Siyasa da Tattalin Arziki.

Ana ɗaukar Taytu Betul a matsayin ɗaya daga cikin shahararrun shugabannin Habasha, mata ce ga Sarkin Sarakuna Menelik II. Ta taka rawa wajen murƙushe ƴan Mulkin Mallaka na Italiya, ita ce kuma ta kafa birnin Addis Ababa.

Wace ce Taytu Betul?

Taytu Betul, wata mace ce ƴar ƙasar Habasha mai kima da daraja wadda tare da mijinta sarkin sarakuna Menelik II suka yi mulkin Habasha daga 1889 zuwa 1913.

Ana tuna ta saboda jajircewarta da adawa da kuma nasarar da ta samu a kan Sojojin Turawan mulkin mallaka na Italiya da kuma ƙarfin ikonta a kotun Sarki.

Ita ce ta zaɓi yankin da a yau ya zama babban birnin Habasha ta kuma sanya masa suna ‘Addis Ababa.’

Wace ce Taytu Betul Kafin ta Zama Sarauniyar Sarakuna?

An haifi Taytu Betul cikin iyalan sarauta masu ƙarfin tasiri waɗanda ke da dangantaka da Daular Sulaimaniya wajen shekarar 1840 ko 1851 a cewar wasu majiyoyi a Debre Tabor wadda ba shi da nisa da Kogin Tana.

An yi mata auren fari ta na yarinya ƴar shekaru 10 da haihuwa, wadda ba abin mamaki ba ne ga yarinya ƴar babban gida a wancan zamani.

An bayyana cewa ta yi aure-aure waɗanda ba ta ji daɗinsu ba kafin daga ƙarshe ta auri mijinta na biyar Sarkin Daular Shewa wadda daga baya ya zama Sarkin Sarakuna Menelik II. A lokacin aurensu ta tara dukiya da kadarori masu yawa.

Ya ya aka yi Taytu Betul ta Zama mai Ƙarfin Faɗa a JI?

Auren Taytu Betul da Menelik II haɗi ne mai ƙarfi kasancewar ɓangarori biyu sun kawo haɗaka da ƙawance a Arewaci da Kudancin Habasha.

Yayin da suka zama Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakunan sun ƙulla ƙawance da sarakuna da dama na yankin wasu ƙawancen lumana wasu kuma bayan an gwabza yaƙi. Sai dai kuma Taytul Betul ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa ba wai ta kasance matar sarki ba kawai, amma ta zama cikin masu bada shawara da kuma cikin mayaƙa.

Masana tarihi sun ce, ana kallon ta daidai da Menelik II kuma a wasu lokutan ta kan zartar da ɗaukar mataki mai tsauri fiye da mijinta.

Da me Taytu Betul ta fi Shahara?

Taytu Betul ta yi fice bisa rawar da ta taka na jagorantar yaƙi a kan Italiya wadda ya haifar da Yaƙin Adwa. An ce, Taytu ta jagoranci runduna ta Mayaƙa 5,000 da Dawaki 600 wajen fafatawa da Italiyawa waɗanda suke ƙoƙarin yi wa Habasha Mulkin Mallaka.

Taytu, ta dage wajen yin adawa da ƙulla yarjejeniya da Italiya wadda aka yi wa laƙabi da yarjejeniyar ‘Wuchale‘ wadda a takarda ta sanya Habasha ƙarƙashin ikon Italiyawa.

A lokacin da Menelik II da Taytu suka afka yaƙi ga Italiyawa, Taytu ta taka muhimmiyar rawa da kuma jagorantar rundunar ta zuwa fagen daga. Ta sami gagarumar nasara a wani wuri da Italiya ta gina a Mekelle inda ta murƙushe Italiyan ta hanyar datse musu hanyoyin samun ruwa.

Shin Taytu Betul Mace ce da ta Fita Daban a Zamaninta?

Habasha ta yi shugabanni mata masu ƙarfin iko, iyaye mata ko matan masu mulki da kuma mata da dama da suka shiga aikin soji – wataƙila ba lallai su ɗauki makamai ba, to amma sun taimaka wa Sojoji wajen girki da share-share da kuma ƙarfafa musu guiwa. Ba kasafai mata suke jagorantar rundunar mayaƙa ba kamar yadda Taytu ta yi.

A wasu bayanai da suka siffanta Yaƙin Adwa, an baiyana ta a matsayin gwarzuwar yaƙi, sai dai babu wata shaida da ta nuna ta ɗauki makami da kanta. Ta iya karatu da rubutu wadda hakan ya sa ta zama ta musamman. Taytu, na son yin wasan dara da kuma waƙoƙi.

ME Ya Faru Bayan Rasuwar Menelik?

A 1909 Sarki Menelik ya sami shanyewar ɓarin jiki. Ta karɓi ragamar gudanar da yawancin ayyuka musamman gudanar da sha’anin mulki.

Bayan wasu lokuta masu hamayya da ita a cikin iyalan Masarauta suka matsa mata lamba ta yi murabus. Wasu masana tarihi sun yi imanin cewar, ta zama mai matuƙar ƙarfin iko wadda ya sa wasu da dama ba sa son ta a kotun Sarki.

Lokacin da Menelik ya rasu a 1913 aka fitar da Taytu daga Fada kuma ƙarfin tasirinta ya shuɗe. Ta rasu a 1917.

Ta ya ya Muka San Abubuwa da Yawa Game da TAYTU BETUL?

Mun sami labari game da ita ta hanyar tarihi na baka da kuma tarihi da aka rubuta sannan kuma da bayanai na hotuna.

Jama’a a kotun Habasha da Jakadun ƙasashen waje da Fursunonin yaƙi na Italiya da kuma wasiƙu da Taytu ta rubuta da kanta sun yi cikakken bayani game da ita.

Wani Injiniya na Switzerland, Alfred Ilg wadda ya yi hulɗa da Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakuna shi ma ya tara bayanai da hotunan sarakunan wadda ya ba da haske a kan rayuwar Fadar.

Madogara

Shawarwarin kimiyya a kan wannan maƙala sun samu ne daga Farfesa Doulaye Konaté, da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Gimbiya Yennenga: Kakar Al’ummar Mossi na Burkina Faso

Daga: Richard Tiéné (ATB/MNA) Gimbiya Yennenga, ta kasance jaruma a fagen yaƙi kuma ƙwararriya wajen hawa Doki. Ta bar tarihi