Al'amuran Yau Da Kullum

An Gano Kayan Da Aka Rina a Zamanin Annabi Dauda

Masana kimiyyar haƙar kayan tarihi ƴan Ƙasar Isra’ila sun gano wani rinin launin Shuni ko “purple” a jikin wani ƙyalle da aka bayyana tun na zamanin Annabi Dauda (A.S) ne.

An bayyana cewa darajar wannan Launi ta fi ta Zinariya, kuma ana danganta shi da Mulki ko Sarauta.

Wannan shi ne karon farko da aka samu ƙyallen Tufafi mai irin wannan Launi da ya samo asali wancan zamanin a yankin.

Wani ƙwararre a Cibiyar Lura da Kayan Tarihi ta Isra’ila, Dr. Naama Sukenik ya danganta shi da “gagarumi kuma muhimmin gano abu ta aka taɓa yi.”

An tono ƙyallen ne lokacin da ake gudanar da aikin haƙa a filin Timna, kimanin kilomita 220 daga Kudancin birnin Ƙudus.

An gano kyallen ne a wani filin haƙa da ake kira ”Slaves’ Hill”.

“A cibiyar adana kayan tarihi, ana danganta kaya masu launin shan-shan-bale da sarauta ko mulki ko malanta,” in ji Dakta Sukenik.

“Ganin cewa kyakkayawan launin ba ya koɗewa, kana yadda samun rinin launin ke da wahalar haɗawa, da kuma yadda ɗan kaɗan ake samunsa daga jikin ƙwanson Dodon-koɗi da dangoginsa, hakan ya sa ake cewa darajarsa ta fi Zinariya tsada.”

An ambaci launin Shuni ko Shan-shan-bale a cikin Yahudawa da na Injila (Bible), da suka haɗa da rigunan da Annabi Dauda, da Annabi Sulaimanu da kuma Annabi Isa suka saka.

Yadin na ƙunshe da rinin launin shunin da aka gano lokacin da ake haƙa a wani fili da ake kira “Slaves’ Hill.”

“Ba tare da ɓata lokaci ba launin ya ja hankalin jama’a, amma mun cika da mamaki cewa da gaske mun samu launin nan da aka sani tun zamanin kaka da kakanni,” in ji Farfesa Erez Ben-Yosef daga sashen kimiyyar haƙar kayan tarihi na Jami’ar Tel Aviv.

Kafin zuwan wannan zamani, a kan samu irin wannan launi ne daga jikin kwanson Dodon-koɗi da halittu dangoginsa, kuma wasu ɓurɓushin aikin ginin tukwane, amma ba a jikin tufafin da aka rina ba.

Sakamakon binciken lokacin wannan ƙyalle ya nuna cewa tun daga kimanin shekaru 1,000 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S), a daidai lokacin mulkin Annabi Dauda (A.S), sai kuma na ɗansa Annabi Sulaiman (A.S).

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An