Al'amuran Yau Da Kullum

Yadda Aka Ƙaddamar da Bikin Baje-kolin Kayayyakin Tarihin Daular Tang

An Ƙaddamar da Bikin Baje-kolin Kayayyakin Tarihi na Zamanin Daular Tang na Ƙasar Sin

Daga: Bello Wang

An ƙaddamar da bikin bajekolin kayayyakin tarihi na zamanin Daular Tang na Ƙasar Sin, ƙarni na bakwai zuwa na goma bayan haihuwar Annabi Isa AS, a gidan adana kayayyakin tarihi na Musee Guimet da ke Ƙasar Faransa.

Shugaban Ƙasar Sin, Xi Jinping, da takwaransa na Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, sun rubuta wasu bayanai, domin a nuna su a wajen bikin.

Cikin bayanin da ya rubuta, Shugaba Xi na Ƙasar Sin ya ce, zamanin Daular Tang wani lokaci ne da Ƙasar Sin ta samu ci gaba sosai, a dukkan fannonin tattalin arziki, da al’adu, da tunani, da dunƙulewar al’ummu.

Saboda haka, ya yi imanin cewa, jama’ar Ƙasar Faransa, da ta sauran Ƙasashen da ke Nahiyar Turai, za su fahimci yanayi mai armashi da ake ciki a lokacin Daular Tang, da gane ma idanunsu abubuwa masu ban sha’awa da ke da alaƙa da al’adun gargajiya na Ƙasar Sin, ta hanyar halartar bikin baje-kolin.

A nasa ɓangaren, Shugaba Macron na Ƙasar Faransa ya rubuta cewa, Gidan Adana Kayayyakin Tarihi na Musee Guimet ya shirya bikin ne don taya murnar cika shekaru 60 da ƙulla hulɗar Diflomasiyya tsakanin Ƙasashen Faransa da Sin.

A cewarsa, wannan bikin baje-koli mai ma’anar tarihi ya nuna yanayi mai kyau da cuɗanyar ƙasashen biyu a fannin al’adu, wadda za ta ƙara taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin kyautata hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An