Dausayin Masoya

Labarin Wasu Masoya Ɗan India da Ƴar Pakistan da Suka Ƙare a Gidan Yari

A watan Janairun 2023, an kama wani Ba’indiye da ya taimaka wa wata ƴar Pakistan da ta shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba ta kuma samu katin shaida na bogi.

Matar Da Ya Taimaka Matarsa Ce

Mulayam Singh Yadav, ɗan shekaru 21 ɗan asalin India da Iqra Jeewani mai shekaru 19 wadda ta fito daga Pakistan sun haɗu ne a intanet shekaru uku baya, daga nan suka fara soyayya, kuma sun fara ne ta hanyar yin wasan Ludo. Amma sun san abu ne mai wuya su kasance tare.

Alaƙa tsakanin India da Pakistan ta jima a matsayin marar daɗi – maƙotan sun yi yaƙi tsakaninsu sau uku tun daga shekarar 1947, lokacin da India ke fafutukar neman ƴanci ita kuwa Pakistan ta ƙirƙiri nata. Wannan ya sanya samun biza tsakanin ƙasashen biyu masu tarihi ɗaya yake da wuya.

A watan Satumbar da ya gabata ne, Mulayam da Iqra suka je Nepal, suka yi aure a can. Daga nan kuma suka tafi Bangalore babban birnin Karnataka inda suka ci gaba da rayuwa.

Rayuwar da suke yi mai daɗi ta koma ta wuya a watan Janairu, inda aka tsare Iqra saboda ta shiga India ba ta hanyar da ta dace ba, shi kuwa aka kama shi saboda aikata laifin zamba cikin aminci da yi wa wani takardun ƙarya da kuma bai wa ɗan ƙasar waje wurin zama ba tare da cikakkun takardu ba.

An mayar da ita Pakistan a makon jiya, shi kuwa an ci gaba da tsare shi a gidan yari da ke Bangalore.

Ƴan uwan Yadav, wanda ke zaune a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin India, sun ɗimauta da kamun da aka yi masa.

“Muna fatan muga sun dawo gida, mun san abin da ke tsakanin India da Pakistan. Amma su masoya ne kawai,” in ji Jeetlal ɗan uwan Yadav.

Ko Ƴan Sanda Sun Yi Kamar Sun Yarda

“Bayan shiga ba bisa ƙa’ida ba da takardun bogi, sai kuma labarin soyayyarsu,” in ji wani babban jami’in ƴan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa.

Masoyan sun yi aure a bara, sai dai ba su ɗauki lokaci su na rayuwa ba tare.

Labarin soyayyar ya samo asali ne a 2020, lokacin kullen annobar Korona.

Yadav ya na aiki a wani kamfanin kwamfuta ne a matsayin jami’in tsaro da ke Bangalore ita kuwa Jeewani ta na karatu ne a wata Jami’a da ke Hyderabad a Pakisatan.

Sun fara wannan soyayyar mai nisa ne bayan sun haɗu a intanet. A lokacin Iqra na shan matsin lamba daga iyayenta na cewa sai ta fito da miji ta yi aure.

Ko da Yadav ya yi mata tayin aure, ta amince ta kuma tashi daga Pakistan ta tafi Dubai daga nan kuma ta shiga Nepal inda suka haɗu. A nan ne suka yi aure a wata Majami’a.

Sai dai Jeewani ba ta da takardun da ake buƙata da za su ba ta damar zama a India, sai ƴan sanda suka ce Yadav ya yi mata katin shaidar zaman India na ƙarya.

A cewar ƴan sanda kullum Yadav mijinta na fita aiki amma ita babu inda take zuwa.

Sai dai ko da yaushe ta na yawan kiran mahaifiyarta ta Manhajar WhatsApp da ke India, wanda hakan ya ja hankalin ƴan sanda suka rinƙa bibiyar sawunta.

“A yanzu babu wani laifi da ake tuhumarta da shi bayan shiga India ba bisa ƙa’ida ba,” in ji mataimakin kwamishinan ƴan sanda na Bangalore, kamar yadda ya shaidawa manema labarai.

Manema labarai ba su iya samun Iqra ba da iyayenta da ke Pakistan domin jin ta bakinsu.

Amma a farkon wannan makon ne mahaifinta ya tabbatar da cewa, ta koma gida kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PTI ya bayyana, sai dai sun ce ba sa son cewa komai kan wannan batu.

Mahaifiyar Yadav ta ce, ta na fatan gwamnatocin ƙasashen biyu za su yi ƙoƙarin sake haɗa ma’auratan biyu domin ci gaba da zamansu na aure.

“Ba mu damu ba kan cewa ita Musulma ce ko ƴar Pakistan ce, kawai abin da muka sani surukarmu ce. Za mu kula da ita yadda ya kamata kamar yadda muke kula da shi.”

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

1 Comment

  1. Avatar

    Muhammad sani

    28/11/2024

    Su mutanen pindiga jukunawa ne?
    Sunanda zumunchi da jukunawa na taraba?

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *