Jami’ai a yankin North East Derbyshire da ke Birtaniya, sun umarci mai zakaran ya biya tarar ne bayan an gano cewa zakaran ya yi cara sama da sau 80 a ƙasa da Awa ɗaya.
Da farko an ba wa Derek Bower umarnin killace zakaran nasa, sai dai daga baya aka yi masa wannan hukunci bayan gaza yin hakan.