Aikin gona shi ne dukkan abin da ya shafi Noma da Kiwo, wanda idan aka faɗaɗa shi zai zama ke nan ya ƙunshi gyaran gona, shuka, Noma, kiwon Dabbobi, Tsuntsaye, Kifaye, da sauran abubuwa.
Wannan fanni na aikin gona, fanni ne mai faɗin gaske kuma mai daɗaɗɗen tarihi a Duniya. Ya na daga cikin sana’o’i na tun dauri. Kuma hanya ce ta samar da cimaka (abinci), Makamashi, Magunguna, dss.
Wannan fanni ya na daga cikin manyan fannonin da suke samar da ayyukan yi a Duniya. Sannan kuma hanya ce ta haɓaka Tattalin Arziƙi.
Wannan rubutu da mai karatu ke karantawa zai ɗan yi ƙarin haske ne game da gundarin Aikin Gona (Agriculture).
MA’ANAR AIKIN GONA
Masana wannan fanni sun fassara wannan fanni na Aikin Gona ta hanyoyi da dama. Akwai Microsoft Encarta (2009) da ya kalle shi a matsayin Kimiyya, da kuma Masana’antar kula da Tsirrai da kuma Dabbobi don amfanin ɗan’adam.
Su kuma Wikipedia (2016), sun siffanta shi da Noman Dabbobi, Tsirrai, Makamashi, Magunguna, da sauran abubuwan da ke taimakawa ɗan’adam ya rayu.
Shi kuwa Farfesa Smith (2009), ya siffanta shi da samar da Abinci, abincin dabbobi, Makamashi, da sauran abubuwan da ake samarwa ta hanyar Noman Tsirrai da Kiwon Dabbobi a hikimance.
RABE-RABEN AIKIN GONA
Wannan fanni na Aikin Gona fanni ne mai faɗin gaske. A saboda haka masana wannan fanni sun rarraba shi ta fuskoki da dama. Daga ciki akwai: Aikin Gona na Zamani (industrialized agriculture), da kuma Aikin Gona na Gargajiya (subsistence agriculture).
Aikin Gona na Zamani (industrialized agriculture): Shi ne aikin gonar da ake amfani da kayayyakin Fasaha waɗanda ka iya zama Inji ko Magunguna don sauƙaƙa harkar Aikin Gona wanda ka iya zama imma dai Kiwo ko Noma. Wannan ita ce hanyar da ke samar da sakamako mai yawa kuma cikin sauƙi. Wato ke nan wannan ita ce aikin gonan da ake yi don samun kuɗaɗen shiga.

Aikin Gona na Gargajiya (subsistence agriculture): Shi ne aikin gonar da ake yi don samar da abincin da Iyalai za su ci. Wato muna iya kallon wannan a matsayin ƙaramar Aikin Gona wacce burinta bai wuce samar da abincin da iyalai za su ci ba. Ba Noma ne na neman Kuɗi ba.

WASU RABE-RABEN KUMA SUN HAƊA DA:
Ƙaramin Kiwo (Nomadic Herding): Shi ne irin kiwon da Fulani Makiyaya suke yi, wacce take hanya ce ta kiwata Dabbobi wacce Makiyaya ke yi ta hanyar yawo da dabbobinsu zuwa gurin da za su samu isasshshen Abinci.

Noma: Shi ne abin da ya shafi noma Tsirrai don samar da Cimaka (abinci) wanda ka iya zama ko dai don a sayar ko kuma a a ciyar da Iyali.
