Masana kimiyya sun soma kula da tsuntsuwar ne tun a shekarar 1956 a lokacin da take da shekaru biyar.
Wata tsuntsuwa wadda masana kimiyya suka yi amanna cewa, ita ce mafi tsufa a Duniya ta saki Ƙwai, kamar yadda masana suka tabbatar.
Hukumar Kula da Kifaye da Namun Dawa ta Amurka ta ɗauki hotonta a wani gandun tsuntsaye da dabbobi da ke Tsibirin Pacific, in da ta ɗauki hoton Tsuntsuwar a lokacin da take zagaye da ƙwan nata.

Ta ƙyanƙyashe ƙwanta na ƙarshe a shekarar 2021 inda aka yi hasashen ta ƙyanƙyashe ƙwayaye fiye da 30 a tsawon rayuwarta.