Kimiyya Da Fasaha

Asalin Kimiyyar Haɗa Magunguna a Musulunci

al-kimiyah = alchemy
al-kuhl = alcohol
al-ambiq = alembic
al-kahli = alkali
al-neel = aniline
al-ithmid = antimony
qirat = carat
al-iksir = elixir
jarrah = jar
juleb = julep
sharab = syrup

Waɗannan kalmomi dukkansu su na da alaƙa da asalin kimiyyar haɗa magunguna, kuma asalinsu na Larabci ne.

A ƙasashen Yamma da Gabas ta Tsakiya, farkon fasahar ilmin haɗa Magunguna da Likitanci gamin-gambizar tunani ne daga Girkawa, Indiyawa, Parisa da Rumawa.

A wancan lokacin duk wani rubutu a kan kimiyyar Magunguna sun shafi Tsirrai da amfaninsu.

A farkon ƙarni na 7th CE, ɗaukakar Turai da Gabas sun yi sanyi don haka sun a buƙatar sabon tunani.

Ɗaukakar Daular Musulunci ta kawo ƙishirwar son iilmi da saita Duniya a kan sabon tsari, musamman ma a fannin Kiwon Lafiya. Bayan ƙarni guda da wafatin Annabi Muhammad (SAW) a shekarar 632 CE, tafiya ta fara yin nisa wajen kawo canji a harkar kimiyyar Magunguna a Fadar Masarautar Umayyad a Dimishƙa.

Dafin Maciji, cizon Karnuka, saran Kunama, dafin Gizo-Gizo da irin illolin da ke jikin Tsirrai su ne suka assasa wannan tafiyar, kuma ayyukan Girkawa irin su Galen da Dioscorides da su aka yi tubali wajen rarrabe Guba da Magani.

A koyaushe mutuwar fuju’a ta faru a gidan Sarauta to ana danganta ta da cin wani abu mai Guba ne. Don haka Masarautar Umayyad ta tashi haiƙan wajen gano yadda za a iya kaucewa cin guba da yadda za a magance matsalar idan ta auku. Yawanci Kimiyyar Magunguna ta fi mayar da hankali kan batun guba da dafi.

Ibn Uthal shi ne Likitan Sarki Mu’awiyah a wancan lokacin, Kirista ne kuma masanin kimiyya.

Ana hasashen shi ne ya kashe Sarki Mu’awiyah a shekarar 667. Shi ma daga ƙarshe ana hasashen kashe shi aka yi ta hanyar ba shi guba.

Abu al-Hakam al-Dimashqi shi ne ya koma Likitan Yazid Halifa na biyu a Daular Umayyad, shi ma Kirista ne.

A zamanin Khalid bin Yazid – ɗan Sarki Yazid sha’awarsa da harkokin kimiyya ya sa ya ɗauko hayar Girkawa masana falsafa daga Misra. Ya biya su lada, suka fassara Littattafan kimiyyar haɗa Magunguna, ilmin Likitanci da ilmin Falaƙi zuwa harshen Larabci. Jabir ibn Hayyan, wanda Turawan Yamma suke kira da Geber ya assasa bincike da faɗaɗa ilmin kimiyyar harhaɗa Magunguna da kimiyyar abubuwa masu rai ta sahihiyar hanya.

A ƙarni na 9th, Daular Abbasid da ke mulki a Bagadaza ta ƙara faɗaɗa aikin fassara Littattafan Girkawa, Indiyawa da Parisa.

Hunayn ibn Ishaq, shi ne ya yi wannan aikin fassarar da tallafin Gwamnati. Shagunan sayar da Magunguna sun yawaita a Bagadaza, har sai da Gwamnati ta fito da tsari da dokoki da makarantun koyon aikin sarrafa magunguna domin a tsaftace harkar.

Manyan masana ilimin kimiyya daga Daular Abbasid su ne Abu al-Fa’id Ohun-Nun daga Misra da Ibn Wahshiyyah, dukkansu sun yi rubutu mai yawa a kan kimiyyar haɗa magunguna da ilmin falaƙi. Amma aikin al-Razi shi ne ya yi fice a lokacin, sun ba da gudunmowa a fannin kimiyya, ilmin haɗa magunguna da ilmin Likitanci.

Sunan mai haɗa magunguna “Saydalani” ita kuma kalmar Saydalani wacce aka aro ta daga yaren Sanskrit ta na nufin; Mai sayar da turaren wuta irin na sandal da kamfur, turaren miski, alam da sauransu.

Al-Aqrabadhin Sabur ibn Sahl shi ne ya wallafa Littafin haɗa magunguna mai sahihan bayanai a kan magunguna da yadda ake haɗa su. Sannan Ibn al-Baytar a ƙarni na 12th wanda aka haife shi a garin Granada wanda ya wallafa Littafi mai ɗauke da bayanan sinadaran magunguna sama da 1,400.

A yau dukkan wata gajiya da ake ci a fannin harkar haɗa magunguna, to Musulunci ne ya samar da ita.

Rubutu: David W. Tschanz
Fassara: Ado Abubakar Bala
AramcoWorld: May/June 2016

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa Daga: Amina Xu An gudanar