Adabi

Matakan Rubuta Ƙagaggun Labarai

Idan aka ce matakan rubuta ƙagaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta ƙagaggun labarai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren waɗannan ƙagaggun labarai, don haka a wannan ɓangare za mu duba ire-iren matakai ko hanyoyin ko tubala da ake amfani da su wajen rubutun.

TUNANI

Abu na farko da mai son rubuta ƙagaggen Littafi na Hausa zai fara tanada shi ne; Tunani. Tunani shi ne babban abu a wajen mai rubuta ƙagaggen Littafi don in babu tunani ko kuma in ba a yi tunanin mai ake so a rubuta ba babu rubutun Littafin gaba ɗaya, dole ne a fara da tunanin abin da ake so a rubuta a cikin littafin.

LABARI

Dole ne mai son rubuta ƙagaggen Littafi ya tanadi labari, wato abin da yake so ya rubuta, shin labarin soyayya ne ko na jarumta ko na yara ko na aljanu ko kuma wani daban? Don yin hakan shi ne zai sa ya san alƙiblar da ya dosa, kuma ya sami sauƙin isar da saƙonsa, in bai tanadi labari ba akwai matsala don ko ya zauna don rubutun in bai san labarin da yake son rubutawa ba, to, abin ba zai yi wu ba.

Shi kuma labarin ba sai mutum ya san komai da komai na cikinsa ba, amma dai zai fi kyau in an san daga inda aka tashi da kuma in da za a sauka, ma’ana; Ka san farkon labarinka da ƙarshensa, amma sauran abubuwan da ke cikin tsakiyar labarin sai ka zo rubutun sannan za ka same su, a lokacin da basirar rubutun take saukowa.

Misali ina so zan taso daga unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna zuwa Kwalejin Koyar da Harkokin Kasuwanci, kuma Sashen Share Fagen Shiga Jami’a, a garin Dutse, don halartar taron ƙara wa juna sani na kwana ɗaya, kuma na san dole zan bi ta kan titin Ahmadu Bello Way kafin in iso garin Dutse. A nan mun san ga inda na baro ga kuma inda nake son zuwa, amma abubuwan da za su faru a hanyar ban sani ba sai na taho sannan zan gani in sun faru. To haka abin yake a rubutu, sai ka zo wajen yin rubutun ne za ka ji abubuwan su na zuwar maka a ƙwaƙwalwa, kuma kana rattaba su a cikin takardarka ko wayarka ko na’urarka ya danganta da irin abin da kake rubutun a jikinsa, Takarda ce ko Kwamfuta ko kuma Waya.

SUNAN LITTAFI

Ya na da kyau mai rubuta ƙagaggen Littafi ya yi wa Littafinsa suna kafin ya fara ko kuma kafin ya gama, domin sanya wa Littafin suna ya na taimakawa mai rubutun labarinsa ya dinga tafiya da sunan Littafin. Wasu lokutan ana samun Littafi da aka gama rubutawa ba a sanya masa suna ba, sai daga baya a zo ana ta kame-kamen yadda za a sanya masa suna, wanda da an ba shi suna tun farko da ba a sami wannan matsala ba, kuma labarin zai fi tafiya da sunan sosai.

LOKACI DA GURI

Ya kamata mai rubuta Littafi ya lura da lokaci da kuma gurin da yake rubutun, abin da ake nufi a lura wajen sanya lokaci, kamar kwanakin wata ko shekaru don ka da a dinga samun rikicewar lissafin shekarun ko watanni, don ana iya samun rikicewarsu in ba a kula ba. Haka ma batun guri, idan kana rubuta Littafi mai bayar da labarin rayuwar Birni ko Karkara, ka tabbata abin da kake rubutawa a cikin labarin Karkara ya na faruwa a Karkara, haka abin da kake rubutawa na game da Birni ka tabbata su na wakana.

BINCIKE

Ya na da kyau a duk lokacin da mai rubutu ya zo yin rubutu a kan wani abu da aka san ya na buƙatar bincike, to a bincika shi don ka da a rubuta shi da ka, yadda zai zo ya ruɗar da mutane musamman ma waɗanda ba su san shi ba. Misali abin da ya shafi Lafiya da Shari’a da Al’adu da kuma Addini.

SINADARAI

Har ila yau, akwai ƙarin wasu sunadarai ko tubala waɗanda idan aka haɗa su yayin rubuta ƙagaggun Littattafai musamman na soyayya sun fi daɗi da armashi, kamar:

  • Sunayen mutanen da suka dace (Taurari)
  • Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta
  • Bayyana ire-iren mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi so
  • Bayyana kyawawan halaye na iyaye da ƴaƴansu
  • Biyayya
  • Fito da abubuwan da Namiji ya fi son Mace ta yi masa
  • Fito da abubuwan da Mace ta fi son Namiji ya yi mata
  • Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya,
    musamman a rayuwar ma’aurata,
  • Yanayin soyayya bayan ta rikiɗe ta zama aure
  • Amfani da kalmomin soyayya masu daɗi da faranta zuciya, dss.

Ko da yake wasu su na ganin a da can ba a cika rubutu kan soyayya ba saboda wasu dalilai kamar yadda a wata gabatarwar da Farfesa M.K.M. Galadanci ya yi a wani Littafi na soyayya a cikin shekarar 1992, ga abin da ya ce;

“Marubutan Hausa na farko ba su cika son yin rubutu kan soyayya ba, wataƙila don gudun zancen Mata da amfani da kalmomin ƙuruciya ko ma ta kai ga yin batsa saboda haka da wuya a sami daɗaɗɗen littafi (kai ko ma rubutacciyar waƙa) kan soyayya. A ƴan shekarun nan marubutan zamani, matasa, sun toshe mana wannan giɓi na Adabin Hausa. Wannan littafi wanda Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya wallafa, ‘Hattara Dai Masoya,’ na ɗaya daga cikin kyawawan misalan irin wannan ƙoƙari” (Galadanci, M.K.M.; 1992: shafi na K).

Wasu kuwa su na ganin babu wani alfanu ma kwata-kwata a cikin littatafan soyayya da ake rubutawa, su a wajen su gwara a dinga rubuce-rubuce a kan Yunwa da Fatara da Talauci da Yaƙe-yaƙe da Annobobi iri-iri, maimakon in ba kai ba sai rijiya. Sannan kuma rubuce-rubucen su na cike da kura-kuran Hausa da rabe-rabenta da kuma ɓata tarbiyyar matasa Maza da Mata, da kuma yin fassara daga Littattafan wasu jinsin mutane waɗanda ba al’adar su ɗaya da ta Bahaushe ba.

Wasu kuwa su na ganin ba labaran soyayya ne suka ishi mutane ba, a’a salon ne ya ishe su in har ya ishe sun.

Ko ma dai ya ya abin yake, wasu su na ganin marubuta ƙagaggun Littattafan Hausa musamman na soyayya sun bayar da tasu gudunmawar wajen bunƙasa da yaɗa Adabin Zamani a Ƙasar Hausa da kuma Duniya baki ɗaya, domin an samar da dubunnan Littattafai a wannan fage, kuma sanadiyyar haka an sami waɗannan abubuwa;

  • Rikiɗewar makaranta Littattafai zuwa ga rubutawa
  • Samuwar sababbin Marubuta
  • Samuwar makaranta Littattafai
  • Samuwar ƙungiyoyin Marubuta
  • Samuwar waɗanda ba Hausawa ba a cikin rubutun Hausa
  • Samuwar Ƙungiyoyi Makaranta Littattafai
  • Samuwar Kantunan sayar da Littattafai masu yawa
  • Zuwan baƙi daga wasu Jihohi da ƙasashe don sayen Littattafai
  • Yawaitar masu bincike a kan Littattafan soyayya (manazarta), da rubuta ta
  • Ƙarfafa danƙon zumunci (a cikin gida da waje)
  • Cusa wa mai sauraro ko mai karatu farin ciki da gusar masa da ɓacin rai
  • Son karatun Hausa da bunƙasa Harshen
  • Cusa sha’awar yin rubutu a zuƙatan matasa Maza da Mata
  • Kyautata zamantakewar Ma’aurata da kuma Masoya ta hanyar karatun Littattafan
    Soyayya
  • Samar da aikin yi ga matasa Maza da Mata har da matan aure
  • Ƙalubalantar auren dole a ƙasar Hausa
  • Yaƙar jahilci
  • Ƙulla hulɗar zumunci tsakanin marubuta da makarantansu, dss.
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Adabi

Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau

Manyan ƴan bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne ƴan jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace.