An kafa shafin intanet na Taskar Nasaba, a ranar Shida ga watan Yuni na shekarar 2021, a wani ɓangare na manyan manufofin yaɗa labarai ta intanet a cikin harshen Hausa, a yayin da Duniya ke ƙara zama dunƙulalliya a fagen sadarwa da yaɗa labarai.
Taskar Nasaba, na bai wa jama’a ingantattun labarai da sanar da su al’amuran yau da kullum da sanya musu karsashi, da ba su damar bayyana ra’ayoyinsu, da kuma gabatar da shirye-shirye game da al’amuran da suka shafi rayuwarsu.
Har ila yau, ta na bayar da labarai da rahotanni masu muhimmanci game da nahiyar Afirka da wasu sassan Duniya.
Taskar Nasaba, ta kuma kasance Cibiyar bincike da nazari a fannonin daban-daban na ilimi.