Jiya Da Yau

Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?

Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al’ummar Duniya, kuma ana ganin tasirinsa a fannonin Siyasa da Kimiyya da fagen rubuce-rubuce.

Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka taɓa gani a doron-ƙasa? Wani fitaccen malamin falsafa ɗan Birtaniya, John Sellars na ganin haka.

Ya ce, ana iya ganin tasirin masanin falsafar ɗan asalin Girka a fagage da dama da irin yadda ya taimaka da tunaninsa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Kama daga fagen Siyasa da Kimiyya, rubuce-rubuce zuwa tunani da dabaru, ana iya ganin tasirin Aristotle a ko’ina.

Ya yi nazarin ilimin halittun cikin ruwa, wani abu da ya haifar da ilimin ‘Biology.’

Ya kuma yi bayanin fannonin tsarin mulki daban-daban, wani abu da ya haifar da ilimin kimiyyar siyasa.

Haka kuma sharhinsa kan iya bayar da labari a cikin Waƙoƙi ya taimaka wajen samar da tsarin Sinima a yau.

Sannan a fannin tunani, dabarunsa a fannin bayar da hujja ya taimaka a kowane fanni kama daga ilimin falsafa zuwa shekarun fasahar zamani.

Farfesa Sellars na Jamai’ar Royal Holloway, da ke Landan, ya sani cewa maganarsa na da ƙarfi. Amma ya dage cewa; tasirin Aristotle ya zarce a yi maganarsa. ”Ya gyara yadda muke tunani”, in ji shi.

Babban Iƙirari

A wata Muƙala da ya wallafa a Mujallar Antigone, Sellars ya yi wani iƙirari da ya ja hankali game da masanin falsafar, in da ya ce, “Aristotle ba kawai babban masanin falsafa ne da ba a taɓa ganin irinsa ba – Shi ne ma mutum mafi muhimmanci da aka taɓa yi a Duniya.”

Wannan babban iƙirari ne, kuma wanda ya faɗaɗa a littafinsa mai suna ‘Aristotle: Understanding the World’s Greatest Philosopher.’

“Plato ne abokina, amma gaskiya ce babbar ƙawata,” a cewar Aristotle. Hoto: Getty Images

“A lokacin da na fara nazarin falsafa, na fahimci cewa, Aristotle ya na da muhimmanci, amma kamar ya na da tsoro,” a cewar Sellars.

“Duk lokacin da na yi ƙoƙari na karanta rubuce-rubucensa, sai nan da nan abubuwa su ɓace min.”

Sai dai bayan lokaci mai tsawo ya fahimci cewa, karantar rubuce-rubucen Aristotle na buƙatar haƙuri da juriya. ”Kana buƙatar sanin yadda za ka karanta rubutunsa,” kamar yadda ya bayyana.

Ya rubuta littafin nasa da nufin taimaka wa masu karatu su san hikimomin Aristotle tare da nuna irin tasirin fitaccen malamin falsafar.

Rayuwar Neman Ilimi

Aristotle da Socrates da Plato ne suka gina babban fagen ilimin Falsafa a Duniya.

An haifi Aristotle a Arewacin Girka, ya na da shekaru 18 ya koma Athens inda ya yi karatu a Makarantar Plato, ya kuma shafe shekaru 20 a matsayin Ɗalibi da kuma Malami a Makarantar.

Duk da girmama Plato, Aristotle ya gina nasa ra’ayoyin. Bayan mutuwar malamin nasa, ya bar Athens zuwa tsibirin Lesbos don karantar yanayi. Ya yi fice a fannin, inda daga baya aka zaɓe shi a matsayin malamin ɗan Sarkin Macedon, wanda ke matsayin Yarima mai jiran-gado, wato Alexander the Great.

A lokacin da Alexander ya fara mulkinsa, Aristotle ya koma Athens inda ya kafa tasa makarantar, mai suna ‘The Lyceum.’

Ya kwashe shekarun ƙarshe na rayuwarsa ya na koyarwa, da rubuce-rubuce da bincike kafin rasuwarsa a lokacin ya na da shekaru 62.

Duk da cewa kaɗan ne daga cikin ayyukansa suka samu wanzuwa, har yanzu su na tasiri, musamman a fagen tunani.

Ƙwararren Masanin Kimiyya

Ba a ilimin falsafa kawai Aristotle ya yi fice ba, ya kasance ɗaya daga cikin masana ilimin kimiyya na farko-farko.

Da jimawa kafin bayyanar na’urorin Microscopes da ilimin Halittu, Aristotle ya nazarci halittun Duniya, inda ya karkasa Dabbobi da Tsirrai a wani mataki da ya bayar da damar samar da fagen ilimin Biology.

Wasu binciken nasa, daga baya ilimi ya tabbatar da kuskure a cikinsu. Amma Sellars ya ce babbar asarar Aristotle ita ce dabarar da ya bi, ya na mai cewa, bincike da hujja suke taimaka wa fahimta.

Kuma waɗannan dabaru har yanzu su ne zuciyar Kimiyya.

Makarantar Lyceum ta Aristotle, ta bayar da Leccoci masu yawa ga jama’a kuma a kyauta, saɓanin Makarantar Plato. Hoto: Getty Images

Gudunmowa a Siyasa da Rubuce-Rubuce

Aristotle ya sanya wasu dabarun ilimi da tunani cikin Siyasa

Ya tattara tare da kwatanta Kundayen Tsarin Mulki na Birane da Ƙasashe daban-daban domin fahimtar dalilin da ya sa wasu Ƙasashen suka ci gaba, wasu kuma suka zama koma-baya.

Wannan hanya da aka tsara bisa doron hujja maimakon ra’ayi, ita ce ta bayar da damar samar da Ilimin Kimiyyar Zamantakewa, wato ‘Social Sciences.’

Haka ma tasirinsa a fannin rubuce-rubuce ba zai misaltu ba. Baya ga Waƙoƙi ya kuma yi nazarin wasannin Girka, tare da karkasa labarai zuwa sassa daban-daban, farko da tsakiya da kuma ƙarshe, wata dabara da masu rubuta Littattafai da masu shirya Fina-finai na yanzu ke amfani da ita.

Ana kallon Aristotle a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka fi tasiri a tarihin Falsafar Musulunci. Hoto: Getty Images

Masanin Dabaru da Falsafa

Ayyukan Aristotle a fagen dabaru na ɗaya daga cikin gagarumar gudunmowar da ya bayar.

Ya ɓullo da ƙa’idar cewa, kowace magana ka iya zama gaskiya ko ƙarya – abin da a yanzu ake kira ‘Law of the Excluded Middle.’

Aristotle ya kuma tunkari manyan tambayoyin rayuwa na: Ta ya ya muke rayuwa?

A cikin littafin Ɗa’a na Nicomachean, ya bayar da hujjar cewa; Mutane na fama a lokacin da suka daidaita hujja da alaƙar zamantakewa da sha’awar ƙwaƙƙwafi game da hankali.

Rayuwa mai kyau, ita ce inda muke samun iko da kanmu, mu shiga cikin al’ummominmu, don neman ilimi.

Tasirin da ba mu Taɓa Gani ba

Sellars, ya yi imanin cewa, fasahohin Aristotle sun zurfafa cikin fasahohin zamani duk da cewa ba za mu iya tantance su duka ba.

“Dabarunsa sun shiga ko’ina, amma muna ɗaukarsu yanzu tamkar namu.” a cewarsa.

Don haka ma iya cewa, Aristotle ne mutumin da ya fi muhimmanci a Tarihi?

Sellars ya ce a ƙarshe, ya rage ga mai karatu ya yanke shawara – shin Aristotle babban mai tunani ne kawai, ko kuwa, kamar yadda Sellars ya yi jayayya, ɗan’Adam mafi mahimmancin tarihi?

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen